Kafafen sada zumunta na yanar gizo sun bazu, sun shiga kowane lungu da sako na duniya. Saboda su kafafen sun kasance hanya mafi sauki wajen aikewa da karban sakonni masu yawa acikin kankanin lokaci.
Ba kamar su facebook da twitter da instagram ba, shi MBLOG anayin shine da layin MTN kuma shi ba'a bukatan data ko kudi idan mutum zaiyi amfani dashi. Haka kuma mafi rinjaye anayin shi kyauta ne, kuma kowace waya tana iyayinsa inde tana iya tura sakon kar ta kwana wato SMS.
Shima MBLOG yana da group da chatting da kuma wajen yin posting, sai de idan zakayi chatting da mutum sai karike username nashi - ba kaman Whatsapp ba wanda shi kawai lambar mutum ake bukata idan zakayi chatting dashi.
MBLOG yana da dadi sosai, saboda shi ba ruwanshi da network 3G ko 4G, domin baya aiki data ko WiFi ko WLAN, shi kawai yana bukatan network wanda zaka iya aika ko karban sakon SMS dashi. Wani abun burgewa shine ana samun takaitattun labarai akan harkokin yau da kullum.
Idan zaka bude MBLOG abun da kake bukata shine layin MTN mai rajista, wanda yake iya aikawa da karban kira da sakon SMS. MBLOG yana aiki akan kowace waya kaman yanda nafada a baya, kuma babu ruwan shi da data, sannan kyauta akeyin sa, amma akanso mutun yana biyan Naira goma(N10) duk bayan dan wani lokaci.
MBLOG gaba daya anayin shine ta hanyar gajeren sako wato SMS, ba'a tura hoto ko waka dashi. Shi iyaka sakon rubutu kawai ake musaya tsakanin masu aiki dashi.
Ga Yanda Akeyi
1. Da farko kashiga wajen rubuta sakon kar ta kwana wato SMS, sai ka rubuta 'Edit' katura shi zuwa '50017'.
Nan take zasu tura ma sakon cewa kayi reply da sunan da kakeso yazama username naka, amma wanda bai wuce harafi ashirin ba, misali Jack.
Misali kanaso kasa 'Nura2019' a matsayin username naka - abun da zakayi shine kawai sai ka rubuta sunan da kakeso, sannan ka turashi zuwa '50017'.
2. Idan sunan da kasa yayi babu wani mai amfani da irinshi, zasu ce kazabi jinsin ka. Mace sai tayi reply da 2 na miji kuma yayi reply da 1.
3. Kana gamawa da jinsi sai kuma kasa sunan garin da kake. Anan sun yi misali da jahar Lagos. To ni ba a Lagos nake da zama ba, sai nasa sunan jahar da nake wato Katsina.
4. Daga nan zasu ce kasa sunan aikin ka ko sana'ar dakakeyi. Anan kuma sunyi misali da teacher wato mai koyarwa. Kaima sai kasa sunan sana'arka nide nasa Student, wato ni dalibi ne.
5. Daga nan kuma zasu ce kasa shekarun ka, sai sukayi misali da shekara ashirin 20. Sai kai ma kasa naka shekarun nide nasa 22 wato shekaru na ashirin da biyu kenan nake nufi.
6. A mataki na biyar wato matakin karshe zasu ce kasa abun da kakeson yi ko kake jin dadin sa. Sai suka bada misali da music da sport, nide nasa Reading, wato karatu. Saboda nafison karatun akan sport da music.
Daga karshe kuma idan komai yayi dai zasu nuna make cewa sunanka yayi dai kuma kagama komai.
Yanda Akeyin Posting
Bayan angama komai wato kabude account. Abu nagaba shine yanda zakayi posting. Idan zakayi posting ka shiga wajen rubuta sako ka rubuta abun da kakeso kayi posting sai ka aikashi zuwa '50017'. Misali ka rubuta 'Barkan mu da war haka' zuwa '50017'.
MBLOG ba'a saka password, kuma ba'a saka email. MBLOG offline akeyin sa wato ba bukatan data da kudi.
Bari mu tsaya anan sai kuma a darasin gaba inda zamu cigaba da bayani akan yanda ake chatting da searching da sauransu. A takaice dai wannan chatting din kyauta ne, kuma ta SMS akeyin sa, lambar wayarka ta MTN kawai zakayi aiki da ita, kuma yana aiki a kowace waya.
Fatan anajin dadin darusan damuke kawowa awannan shafin. Ahuta lafiya mun gode da kawo mana ziyara da kuke yi a kullum ba dare ba rana. ;)

Post a Comment