A darasin da ya gabata mun dakko bayani akan yanda ake bude MBLOG, kuma har munyi nisa a cikin bayanin sai muka yanke shawarar raba wannan darasin gida biyu, wato na daya da na biyu. Kuma munyi alkawari akan cewa zamu cigaba daga inda muka tsaya.
Saboda haka yanzu basai mun tsaya mun bata lokaci akan gabatarwa ba. Bayanin yanda akeyi yana kasa, sannan kuma yau zamu dakko bayanin daga farko, wato daga kan yanda ake saka username, daga baya muyi bayanin wasu bangarori masu mahimmaci.
Domin seta username kaje wajen rubuta sako, ka shiga ka rubuta 'Edit' ka turashi zuwa '50017' kaman yanda mukayi bayani a darasin daya gabata. Kana turawa nan take zasu turo maka sakon cewa kayi reply da sunan da kakeso a matsayin username naka. Suna turoma wannan sakon kayi gaggawar rubuta username naka ka aika musu.
Kasani lokacin da ka aika sakon Edit anaso nan take kayi reply da sunan ka. Idan kuma bakayi reply da username naka ba, bayan lokaci kadan zasu turo maka sakon cewa lambobi bakwai na karshen lambarka shine username naka.
Kasani kana aika sakon Edit zuwa '50017' anaso nan take kayi reply da username naka. Misali kanaso kasa 'Nura8080' a username naka, to a take akeso kayi reply da 'Nura8080'.
Idan kuma akwai mai wannan sunan dakasa nan take zasu turo maka sakon cewa 'Sorry, the name 1 exists. Please input another name. Thanks.' ma'ana sunan dakasa wani yariga yayi amfani dashi.
Idan kuma sunan yayi dai dai wato babu wanda ya rigaka amfani dashi, ka cigaba da rajista kaman yanda mukayi bayani a darasin mu na baya. Idan kuma komai yayi dai dai, sai ka cigaba dayin rajistar ka kawai.
Yanda Ake Chatting
Bayan kagama rajista yana da kyau kasan yanda ake yin chatting dashi. Idan zakayi chatting kawai username na mutum zaka haddace. Bayan ka haddace username din sai kaje wajen rubuta sako ka rubuta sakon ka. Misali ace zakayi chatting da mai suna 'Nura2019' abun da zakayi shine ka rubuta sunan mutum da alamar hash wato # a karshe.
Ga yanda akeyi, ka rubuta Nura2019# Aslm, barka da safe ka turashi zuwa '50017', nan take mai wannan sunan zaiga sakon ka. Shima idan zaiyi maka reply yanda kayi ka aika masa sakon haka shima zaiyi.
Yanda Ake Searching
Yanda ake searching na abokai a dandalin MBLOG ya banbanta da yanda ake searching a Facebook da sauran shafukan sada zumunta. Domin a wadancan shafukan kawai sunan wanda kakeso kayi searching zaka rubuta. Sai su baka jerin sunayen da sukayi kusan kama da abun da ka rubuta.
Sabanin sauran dandalin sada zumunta, idan zakayi searching na abokai a MBLOG kawai sako zaka aika dauke da wani harafi da lamba wato 'F3' zuwa '50017'. Nan take zasu yi maka reply da sako dauke da sunan wani ko wata.
Posting
Mutane da suke amfani da dandalin sada zumunta, sukan rubuta wasu bayanai da kowa zai iya gani ya karanta, kuma ya baiyana ra'ayinshi. Hakama a MBLOG ana yin posting, kuma abokan ka zasu gani suyi like ko sharing, amma ba'a comment.
Kana zaune kawai zakaji wayarka tayi kara kana dubawa zakaga wani abokin ka a MBLOG yayi posting. Sai ka karanta abun daya rubuta idan ya burgeka zaka iya sharing nashi ko liking.
Idan zakayi sharing na post din da mutum yayi zuwa ga abokan ka, yanda zakayi shine kana ganin sakon posting din yazo inbox naka, nan take kawai kayi reply da harafin F. Abokan ka zasuga kayi sharing na wannan sakon.
Idan kuma kanaso kayi liking na post din ne sai kayi reply da harafin V zuwa '50017' shima nan take zasu tura masa sakon wane wane mai suna kaza yayi liking na abun da ka rubuta. Kuma kaima nan take za'ayi maka sako cewa kaine na farko, ko na biyu ko na uku a cikin wadanda sukayi liking na posting.
Haka kuma akwai NEWS wato labarai wanda ake turowa mutane kai akai, amma idan mutum yana biya anfi aiko masa da sakonnin labaran. Da wannan tsarin aiko labarai su kamfanin MTN din suke samun kudi da saura talle da sukeyi acikin sa.
A takaice dai MBLOG dandaline na sada zumunta ga masu kana nan wayoyi. Idan zakayi shi baka bukatar data ko kudi acikin layinka na MTN. Bashi da wahala yana saukin tafiyar wa da budewa. Mun gode da kawo mana ziyara wannan shafin a huta lafiya.

إرسال تعليق